aminiyatrust Profile Banner
Aminiya Profile
Aminiya

@aminiyatrust

Followers
106K
Following
567
Statuses
44K

Sahihin Shafin Jaridar Aminiya. Jaridar Hausa Ta Rukunin Kamfanin Media Trust; Mamallakin Jaridar Daily Trust, Trust TV Da Kuma Trust Radio.

Abuja, Nigeria
Joined July 2014
Don't wanna be here? Send us removal request.
@aminiyatrust
Aminiya
3 hours
Ana ci gaba da samun rahotannin cewa ɓata-gari na far wa al’umma a yankuna da dama a Jihar Kano. A ganinku ta wace hanya za a iya maganin wannan lamari?
Tweet media one
1
0
1
@aminiyatrust
Aminiya
4 hours
Ƙungiyar Izalah karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau ta buɗe sabon gidan Rediyo wanda aka sanya wa sunan Sheikh Abubakar Giro Argungu Radio a garin Kalgo da ke Jihar Kebbi.
Tweet media one
0
1
2
@aminiyatrust
Aminiya
9 hours
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji a Jihar Zamfara.
0
1
11
@aminiyatrust
Aminiya
10 hours
An gurfanar da mutum uku ’yan uwan juna da suka yi wa wata matar aure duka da karaya uku, suka kakaɗa wa mijinta dukan kawo wuƙa a Jihar Kano.
0
0
0
@aminiyatrust
Aminiya
12 hours
Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar tarwatsa 'yan ta'adda masu biyayya ga Bello Turji a Jihar Zamfara a babbar mafakarsu, tare da ceto mata da yaran da suka sace kafin su tsere.
Tweet media one
0
0
0
@aminiyatrust
Aminiya
12 hours
An gurfanar da Fira Ministan Isra'ila, Banjamin Netanyahu, a kotu kan zargin sa da karbar cin hanci.
0
0
0
@aminiyatrust
Aminiya
13 hours
An kama ɗan fashin da ya yi wa ɗalibai mata uku a Jami'ar Jihar Kwara fyade tare da yunƙurin kisa.
0
2
9
@aminiyatrust
Aminiya
13 hours
Kwamishinan ’yan sanda Abuja ya ce rundunar tana neman ’yan bola-jari ruwa a jallo.
0
0
2
@aminiyatrust
Aminiya
1 day
Shugaban mulkin Soji na Kasar Nijar ya kafa wani kwamiti da wakilan kasar zasu shata wa'adin rikon kwarya don sanin inda makomar lasar ta dosa
Tweet media one
0
2
23
@aminiyatrust
Aminiya
2 days
Ganduje ya bayyana haka ne a yayin wata ziyarar aiki da ya kai Jihar Anambra.
Tweet media one
0
0
10
@aminiyatrust
Aminiya
2 days
HOTUNA: Yadda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya halarci taron yaye ɗalibai da aka yi a Kwalejin Ilimi da Shari'a ta Yusuf Bala Usman da ke garin Daura.
Tweet media one
Tweet media two
Tweet media three
0
0
0
@aminiyatrust
Aminiya
2 days
Ministan Ayyuka a Najeriya, David Umahi ya bayyana cewa gwamnati za ta kafa shingen karɓar haraji a hannun direbobi da zarar ta kammala aikin babban titin Kano zuwa Abuja. Ministan ya ce karɓar kuɗin ya zama dole domin za a riƙa amfani da kuɗin wajen kula da titin.
Tweet media one
0
1
1
@aminiyatrust
Aminiya
2 days
Kwamitin da Shugaba Tinubu ya sa aka kafa don binciken kan mutanen da ke zaune a Najeriya ne ya gano haka, inda ya ce a yanzu sama da mutum 6,000 ne ’yan asalin Jamhuriyyar Nijar suka mallaki lambar NIN.
Tweet media one
0
1
11
@aminiyatrust
Aminiya
2 days
HOTUNA: Yadda aka yi rusau a kasuwar Yankeke da ke bakin Asibitin Koyarwa na garin Jos da ke Jihar Filato. Hoto: Ado Abubakar Musa
Tweet media one
Tweet media two
Tweet media three
Tweet media four
1
2
15
@aminiyatrust
Aminiya
2 days
Cibiyoyin tara madara na zamani guda 100 da aka samar a Jihar Kano na adana lita miliyan 146 na madara a shekara
0
0
4
@aminiyatrust
Aminiya
2 days
HOTUNA: Yadda Hamas ta miƙa wa Isra'ila sojoji uku da ta tsare bayan bangarorin sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Tweet media one
Tweet media two
Tweet media three
0
0
0
@aminiyatrust
Aminiya
2 days
An dakatar da Dagacin Karagawal da ke Jihar Gombe, Usman A. Bello, daga kujerarsa, har sai an kammala bincike kan zargin da ake masa da amfani da adda ya sassari wani maraya har sau bakwai.
0
0
1
@aminiyatrust
Aminiya
2 days
Bello a yayin wata hirarsa da BBC ya ce bai ma san ko faɗan da ake zargin suna yi da gaske ne kamar yadda mutane ke ta yayatawa. Ya ce ba ya tsammanin suna rigima da juna don bai taɓa jin kowannensu ya fito ya zagi ɗayan a wurinshi ba.
Tweet media one
0
0
1
@aminiyatrust
Aminiya
2 days
Matasan da suka tsere daga rikicin Boko Haram a Jihar Borno sun bayyana yadda suka samu karatu a sansanin ’yan gudun hijira, tun daga sakandare har suka zama likitoci da injiniyoyi lauyoyi da sauransu.
0
0
0
@aminiyatrust
Aminiya
2 days
Ministan Ilimi Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana yayin da yake ƙarin haske game da sauya tsarin karatun sakandare a Najeriya inda ya ce har ba a kai ga yanke hukunci ba, ana kan shawarar gabatar da ƙudirin ne domin ya zama doka.
Tweet media one
0
2
10